Isa ga babban shafi
Wasanni

An fara sauraron karar tuhuma mafi girma a fagen wasanni

An fara saurar karar wasu tsaffin manyan jami’ai a hukumomin kwallon kafa na kasashen kudancin Amurka, dama na hukumar FIFA, a karkashin tuhuma mafi girma da aka taba gani a tarihin kwallon kafa a matakin duniya.

Tambarin hukumar lura da wasan kwallon kafa ta Duniya, FIFA, wanda ke Hedikwatarta a birnin Zurich, na kasar Switzerland
Tambarin hukumar lura da wasan kwallon kafa ta Duniya, FIFA, wanda ke Hedikwatarta a birnin Zurich, na kasar Switzerland REUTERS/Arnd Wiegmann/Files
Talla

Bayaga jami’an guda uku, masu gabatar da kara a birnin New York inda ake sauraron shara’ar, sun kuma bayyana sunayen wasu jami’a hukumar FIFA 42, da ake zargi da aikata laifuka daban daban har 92, sai kuma wasu laifukan 15, da suka shafi cin hanci da rashawa da ake zargin jami’an da aikatawa, inda sukai sama da fadi da dalolin Amurka miliyan 200.

Masu gabatar da karar na hukumar FIFA sun shigar da karar ce tun a shekarar 2015, amma sai a yanzu aka fara sauraronta gadan gadan.

Daga cikin jami’an da aka gurfanar da suka rike mafi kololuwar matsayi akwai Jose Maria Marin mai shekaru 85, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil, sai kuma tsohon mataimakin shugaban hukumar FIFA Juan Angel Napout mai shekaru 59, da kuma Manuel Burga, wanda a baya ya jagoranci hukumar wasannin kasar Peru har zuwa shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.