Isa ga babban shafi
Wasanni

Mun tanadi matakai masu tsauri kan wariyar launi - Infantino

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino, ya sha alwashin daukar mataki mai tsanani kan wadanda aka samu da lafin furta kalaman cin zarafi ko nuna wariyar launin fata, yayin buga wasannin gasar cin kofin duniya da za’a yi a Rasha, cikin shekara mai kamawa.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. REUTERS/Hannah McKay
Talla

Infantino ya ce gasar cin kofin duniyar da ke tafe, zata zama ta farko da za’a bai wa alkalin wasa damar dakatar da wasa ko kuma soke shi, muddin aka samu wani da ya furta kalaman nuna wariya ko cin zarafi, a tsakanin ‘yan wasa ko daga bangaren ‘yan kallo.

Matsalar nuna wariyar launin fata a Rasha ta yi kamari nedaga shekara ta 1991, a lokacin da ‘yan wasa daga kasashe daban daban suka fara kwarara zuwa kungiyoyin da ke kasar.

Dan wasan gaba na kasar Brazil Hulk da ya taimakawa kungiyar Zenit Saint Petersburg da ke Rasha kammala gasar kwallon kafa ta kasar a mataki na 2, cikin shekarun 2012 da kuma 2016, ya ce kusan a kowane wasa da ya buga, sai da ya ji, ana tsokanarsa da sunan biri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.