Isa ga babban shafi
wasanni

Morata ba zai buga wasan Chelsea da Huddersfiled ba

Dan wasan gaba na Chelsea Alvaro Morata ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Huddersfiled ba a yau a gasar firimiya sakamakon ciwon baya da yake fama da shi kamar yadda kocin kungiyar, Antonio Conte ya tabbatar.

Alvaro Morata.
Alvaro Morata. REUTERS/Giorgio Perottino
Talla

Sai dai a bangare guda, Danny Drinkwater ya dawo daga jinyar zazzabin da ya yi fama da shi kuma har ya fara atisaye a ranar Lahadin da ta gabata.

Sai dai a cewar Conte, ga alama dan wasan bai gama watstsakewa yadda ya kamata ba.

Chelsea wadda ta lashe kofin firimiya a bara, na mataki na uku a teburin gasar firmiya kuma akwai tazarar maki 14 tsakaninta da Manchester City mai jan ragamar teburin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.