Isa ga babban shafi

Najeriya ta fice daga gasar kwallon kwando ta kungiyoyin nahiyar Afrika

Kungiyoyi guda biyu da ke wakiltar Najeriya a gasar kwallon Kwando ta kungiyoyin nahiyar Africa da ke gudana a kasar Tunisia sun fice daga gasar bayan rashin nasarar da suka yi a wasannin na karshe a matakin rukuni.

Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyoyin kwallon kwando na Pillars da Gombe Bulls da suka wakilci Najeriya a gasar kwallon kwando ta kungiyoyin nahiyar Africa da ke gudana a Tunisia.
Wasu daga cikin 'yan wasan kungiyoyin kwallon kwando na Pillars da Gombe Bulls da suka wakilci Najeriya a gasar kwallon kwando ta kungiyoyin nahiyar Africa da ke gudana a Tunisia. completesportsnigeria
Talla

Kungiyar Kano Pillars ta yi rashin nasara ne a wasan da ta fafata da takwararta ta City Oilers mai wakiltar kasar Uganda, inda Oilers suka lallasa Pillars din da kwallaye 95 da 86.

Sai kuma kungiyar ASB Mazembe mai wakiltar kasar Congo ta lallasa kungiyar kwallon Kwando ta Gombe Bulls ne da kwallaye 67 da 47.

Pillars ta kammala wasannin matakin rukuninta na A kenan a matsayi na biyar da maki 6, bayan samun nasara a wasa daya kawai daga cikin 5 da ta fafata.

Ita kuwa kungiyar Gombe bulls ta kammala wasannin rukunin ne a matsayi na 6 da maki 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.