Isa ga babban shafi
Wasanni

Giggs na dab da fara horar da tawagar Wales

Tsohon dan wasan Manchester United, Ryan Giggs na shirin karbar aikin horar da tawagar kwallon kafa ta Wales a kan kwantiragin shekaru hudu.

Ryan Giggs
Ryan Giggs REUTERS/Darren Staples
Talla

Hukumar kwallon kafar Wales za ta gudanar da taron manema labarai a yammacin yau Litinin a birnin Cardiff, in da a hukumance za ta kaddamar da Giggs a matsayin sabon kocin tawagar kasar.

Tsohon dan wasan zai maye gurbin Chris Coleman wanda ya koma horar da kungiar kwallon kafa ta Sunderland a cikin watan Nuwamban bara.

Hukumar kwallon kafar kasar ta jima tana son kulla kwantiragi da Giggs don horar da ‘yan wasanta da suka gaza samun gurbi a gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.