Isa ga babban shafi
wasanni

Wigan ta karya lagwan Manchester City

Kungiyar kwallon kafa ta Wigan Athletic ta karya lagwan Manchester City da ke kokarin lashe kofuna hudu kai tsaye a bana ba tare da wani cikas ba.

Magoya bayan Wigan sun fantsama cikin filin wasa don murnar doke Manchester City
Magoya bayan Wigan sun fantsama cikin filin wasa don murnar doke Manchester City REUTERS
Talla

Karamar kungiyar ta Wigan ta samu nasarar ne akan Manchester City da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi a jiya a gasar cin kofin FA.

Will Grigg ne ya jefa kwallon daya tilo a minti na 79 bayan alkalin wasa ya bai wa Fabian Delph na Manchester City jan kati a dai dai lokacin da wasan ya yi zafi.

Saboda tsananin murna, sai da magoya bayan kungiyar suka fantsama cikin filin wasan bayan kammala fafatawar ta jiya.

Sai dai hoton bidiyo ya nuna yadda magoya bayan Wigan din suka rika tinkarar ‘yan wasan Manchester City har ta kai ga bukatar Sergio Aguero ya kare kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.