Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ba zai kara da Espanyol ba saboda wasansu da PSG

Kochin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane ya ce Cristiano Ronaldo ba zai halarci wasan da kungiyar za ta fafata da Espanyol ba a yau karkashin gasar Laliga da ke ci gaba da gudana.

Wannan ne dai karo na biyu, da Zidane din ke ajje Ronaldo cikin wasanni uku da suka buga a baya-bayan nan.
Wannan ne dai karo na biyu, da Zidane din ke ajje Ronaldo cikin wasanni uku da suka buga a baya-bayan nan. Ahmed Jadallah/Reuters
Talla

Zidane wanda ya fitar da jerin ‘yan wasa 19 da za su fafata ba tare da sunan zakaran kwallon duniyar ba, ya ce Cristiano Ronaldo zai huta ne don samun cikakkiyar damar nuna bajinta a wasan da za su kara da PSG nan da mako guda.

Sai dai kuma ‘yan wasa irinsu Gareth Bale da Karim Benzema suna cikin tawagar da za su kara da Espanyol din a yau haka zalika za su kara da PSG a watan mai kamawa.

A cewar Zidane dole ne a bai wa Ronaldon cikakkiyar damar hutawa la’akari da wasan da ke gabansa.

Wannan ne dai karo na biyu, da Zidane din ke ajje Ronaldo cikin wasanni uku da suka buga a baya-bayan nan, ciki kuwa har da na ranar larabar da ta gabata tsakaninsu da Leganes da suka yi nasara da ci 3 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.