Tawagar FIFA ta isa Moroko
Kwararru daga FIFA sun isa a Moroko da sanyin safiyar yau Talata domin tantance shirin da kasar ke yin a daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya.
Wallafawa ranar:
A kasar Moroko an bayyana cewar tuni da mambobin tawagar Hukumar kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA suka sauka a kasar domin aikin tantancewa da za’a yi a cikin kwanaki 3 bisa tabbacin ko kasar da ke a yankin Arewacin Afruka ta iya yin shirin karbar bakuncin wasar gasar kwallon kafa da ake shirin yi a shekarar 2026.
Mambobin kwamitin su 5 na sirin fara aikinsu ne yau Talata inda za su ziyarci filayen wasanni, da da kayan horasda ‘yan wasa, da kuma wurarenda aka diba domin gudanar da wasannin kazalika da cibiyoyin watsa labarai dangane da gasar da za’a gudanar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu