Isa ga babban shafi
Wasanni

Bayern Munich zata kece raini da Real Madrid a Allianz Arena

A yau Laraba za’a ci gaba da gasar cin kofin zakarun nahiyar turan, inda za’a fafata tsakanin Real Madrid da Bayern Munich a filin wasa na Allianz-Arena da ke Jamus.

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo yayin fafatawa da 'yan takwarorinsa ba Bayern Munich, Mats Hummels da Xabi Alonso a filin wasa ba Santiago Bernabeu da ke Madrid, ranar 18 ga watan Afrilu shekara ta 2017.
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo yayin fafatawa da 'yan takwarorinsa ba Bayern Munich, Mats Hummels da Xabi Alonso a filin wasa ba Santiago Bernabeu da ke Madrid, ranar 18 ga watan Afrilu shekara ta 2017. Reuters
Talla

Sau 24 ana fafata wasa tsakanin Real Madrid da Bayern Munich, Bayern ta samu nasara a wasanni 11 inda ta zura kwallaye 36 a ragar Madrid.

Real Madrid ma dai sau 11 tana lallasa Bayern Munich a wasanni 11 tare da zura kwallye 37 a ragar ta, yayinda kuma ragowar wasanni biyu da suka tashi kunnen doki.

Wasan yau da za’a buga tsakanin Madrid da Bayern shi ne na 25, wanda ya sa shi zama wasan da aka fi yawan haduwa tsakanin wasu kungiyoyi biyu a gasar Zakarun nahiyar turai.

Karo na bakwai kenan kuma Real Madrid ke fafatawa da Bayern München a wasan kusa dana karshe a gasar zakarun turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.