Mourinho yayi nadamar rashin kyakkyawar alakarsa da Wenger
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho, ya bayyana yin nadamar yadda a wasu lokuta ya rika sukar takwaransa na Arsenal Arsene Wenger, tare da nuna masa wasu halaye da ke fayyace tsantsanr adawar da ke tsakaninsu.
Wallafawa ranar:
Mourinho ya bayyana nadamar ce, yayin da yake shirin tunkarar wasan da zasu fafata da Arsenal a filin wasa na Old Trafford ranar Lahadi mai zuwa.
Tun a shekarar 2004 aka fara hamayya tsakanin masu horarwar biyu, bayan da Mourinho ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan Chelsea.
A bayan dai Mourinho yana bayyana Wenger a matsayin kwararre wajen samun rashin nasara, yayinda shi kuma Wenger ke kiran Mourinho da sunan sakarai.
A watan Oktoban shekara ta 2014, masu horarwar, wato Wenger da Mourinho sun kusa baiwa hammata iska a wani wasa da aka buga tsakanin Chelsea da Arsenal, daya daga cikin batutuwan da a yanzu Mourinho ke bayyana nadama akan faruwarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu