Isa ga babban shafi
Wasanni

Salah ya kafa tarihin lashe kyautar marubuta wasanni

Muhammad Salah dan kasar Masar da ke kungiyar Liverpool, ya lashe kyautar kungiyar marubuta labarin wasanni, ta zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na wannan kakar wasa ta 2017/2018.

Dan wasan kungiyar Liverpool Mohamed Salah.
Dan wasan kungiyar Liverpool Mohamed Salah. REUTERS/Andrew Yates
Talla

Manbobin kungiyar marubuta wasannin 400 ne suka kada kuri’a inda Salah mai shekaru 25 ya zama dan nahiyar Afrika na farko a tarihi da ya samu lashe wanna kyauta tun bayanda aka fara bayar da ita a shekarar 1948.

Kwallaye 43 Muhammad Salah ya ci a dukkanin wasanni 48 da ya buga cikin kakar wasa ta bana, a matakin kasa da kuma kungiya.

Kevin De Bruyne na kungiyar Manchester City ne ke biye da Salah a matsayin mafi kwazo, a zaben na marubuta labarin wasannin, yayinda Harry Kane na Tottenham ya ke a matsayi na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.