Isa ga babban shafi
wasanni

Ronaldo na da lafiyar da zai buga wasansu da Liverpool - Zidane

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinadine Zidane, ya ce Cristiano Ronaldo ya shirya tsaf don tunkarar wasan karshe na lashe kofin zakarun Turai da zai gudana ranar Asabar 26 ga watan nan, wato nan da kwanaki 8 masu zuwa.

Ronaldon dai yanzu haka ya na fama da gurdewa a kwaurinsa sakamakon raunin da ya samu yayin faftawarsu da Barcelona matakin da wasu ke ganin ba lallai ya iya abin kirki a wasansu da Liverpool ba.
Ronaldon dai yanzu haka ya na fama da gurdewa a kwaurinsa sakamakon raunin da ya samu yayin faftawarsu da Barcelona matakin da wasu ke ganin ba lallai ya iya abin kirki a wasansu da Liverpool ba. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Zidane din ya kuma tabbatar da cewa Ronaldon zai taka leda a wasan da za su kara da Villareal gobe asabar a gasar La Liga, wasan da a baya ake rade-raden Ronaldon ba zai buga ba kasancewar yana shiryawa wasan karshe na lashe kofin zakarun Tura.

A wasu lokutan Zidane din kan ajje Ronaldon a benci musamman idan yasan akwai wani wasan da yafi wannan muhimmanci a gaba, kamar dai salon da ya yi amfani da shi wasanninsu da Malaga, Las Palmas da kuma Espanyol duk dai a gasar La Liga la’akari da yadda suka zo gab da wasu wasanni na cin kofin zakarun Turai, matakin kenan da ake ganin ya haddasa musu koma baya a gasar ta La Liga.

Ronaldon dai yanzu haka ya na fama da gurdewa a kwaurinsa sakamakon raunin da ya samu yayin faftawarsu da Barcelona matakin da wasu ke ganin ba lallai ya iya abin kirki a wasansu da Liverpool ba.

Har yanzu dai Madrid din tana da damar kasancewa ta biyu a gasar ta Laliga musamman idan ta yi nasara a wasansu da Villareal din ita kuma Atletico ta yi rashin nasara a hannun Eibar har gida, kana kuma ta lallasa Atleticon, ko da ya ke dai abu ne mai wuya musamman ganin yadda Atleticon ke bude wuta a wannan karon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.