Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea bata cancanci lashe kofin gasar FA ba - Mourinho

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho ya ce Chelsea bata cancanci nasarar lashe kofin gasar FA da ta yi ba.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

A ranar Asabar aka buga wasan karshe na gasar ta FA inda Chelsea ta samu nasara akan United da 1-0, a filin wasa na Wembley, bayan samun damar bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Bayan kammala wasan ne Mourinho ya zargi ‘yan wasan Chelsea da kin sakin jiki su buga wasa, a maimakon haka suka tsare gida da kimanin ‘yan wasa tara kamar yadda ya bayyana.

A cewar Mourinho salon da Chelsea ta bi wajen samun nasara a wasan ya sa ko kadan bata cancanci lashe kofin na FA ba.

Kungiyar Chelsea ta kare gasar Premier a matsayi uku, maki 30 tsakaninta da Manchester City da ta lashe kofin kakar wasa ta bana a Ingila, yayinda Manchester United ke a matsayi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.