Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta sauya shawara akan Arteta

Har yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana kan nazarin yanke shawarar wadda zai tabbata magajin tsohon mai horar da ita Arsene Wenger, bayan kawo karshen aikinsa na tsawon shekaru 22.

Tsohon mai horar da kungiyar Paris Saint-Germain Unai Emery.
Tsohon mai horar da kungiyar Paris Saint-Germain Unai Emery. Reuters
Talla

A makon da ya gabata aka rawaito cewa tsohon dan wasan kungiyar Mikel Arteta, wanda a yanzu yake matsayin maitaimakin mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola, ake kyautata zaton zai maye gurbin na Wenger.

Sai dai bayanai daga majiyoyi da dama, na cewa tsohon mai horar da kungiyar Paris Saint-Germain Unai Emery, ake sa ran zai karbi ragamar horar da ‘yan wasan na Arsenal, a maimakon Arteta da aka ambata a makon da ya gabata.

Emery mai shekaru 46, ya jagoranci PSG lashe kofin gasar Ligue 1 ta Faransa daya, da kuma wasu kofunan kalubalen kasar guda hudu cikin shekaru biyu da ya shafe yana horar da kungiyar, kafin yanke shawarar ajiye aikinsa a farkon wannan wata.

Masana wasanni hadi da magoya bayan Arsenal a makon da ya gabata sun yi ta muhawara akan cancantar tsohon dan wasan kungiyar Mikel Arteta a matsayin mai horar da ita, kasancewar wasu na kallon bashi da kwarewa da ya kamata a bashi jagorancin yayinda wasu ke ganin sai an gwada akan san na kwarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.