Rasha zata girke na'urori don tabbatar da tsaro a filayen wasanni
Rasha zata girke na’urori a filayen da za a buga wasannin gasar cin kofin duniya, irin wadanda da aka yi amfani da su a yake-yaken kasashen Syria da Ukraine, don kare filayen daga yiwuwar kai hare-haren ta’addanci musamman ta hanyar amfani da jirage marasa matuki ko mai layar zana.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Batun samar da cikakken tsaro dai shi ne kan gaba wajen masu shirya yadda gasar cin kofin duniyar zata gudana a kasar ta Rasha daga 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli.
Rasha ta fuskanci wasu hare-haren kunar bakin wake tun bayan da ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar ta bana a shekarar 2010, hare-haren da ta dora alhakinsu kan wasu kungiyoyin mayaka da ke arewacin kasar masu alaka da kungiyar IS.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce amfani da na’urorin ba zai tsaya a filayen wasanni 12 da za a yi amfani da su ba kadai, za a girke na’urorin a dukkanin filayen atasaye da kuma otal ko masaukan da ‘yan wasa na kasashen 32 zasu yi amfani da su, a iya tsawon lokacin da zasu shafe zaune a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu