Roland Garros: Saharapova ta sha kaye mafi muni cikin shekaru 6
Garbine Muguruza ‘yar kasar Spain samu kaiwa ga zagayen kusa da na karshe a gasar kwallon tennis ta French Open ko Rolland Garros da ke gudana a Faransa.
Wallafawa ranar:
Muguruza shahararriyar ‘yar kwallon tennis ta 3 a duniya, ta samun nasarar ce, bayan da ta lallasa Maria Sharapova ta Rasha da kwallaye 6-2, da kuma 6-1, a wasan da suka fafata a ranar Laraba.
Wannan rashin nasara ita ce mafi muni da Sharapova, ‘yar kwallon tennis ta 30 a duniya ta taba fuskanta cikin sama da shekaru 6.
A ranar Asabar mai zuwa, Garbine Muguruza wadda ta taba lashe kofin gasar Roland Garros din a shekarar 2016, zata fafata wasan kusa da na karshen ne da Simona Halep ‘yar kasar Romania kuma lamba daya a fagen kwarewar kwallon tennis a duniya ajin mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu