Masoya na ci gaba da yi wa 'yan wasan Senegal jinjina
Masoya kwallon kafar kasashen Afrika daga sassan duniya na ci gaba da jinjina wa bajintar da ‘yan wasan Senegal suka yi, a wasan da suka samu nasara kan Poland da kwallaye 2-1, inda suke cewa ba shakka Senegal da fidda nahiyar Afrika kunya a gasar cin kofin duniyar ta bana.
Wallafawa ranar:
Kafin wasan na ranar Talata, Senegal ce mai wakiltar nahiyar Afrika daga cikin kasashe 5, da ba a samu nasara akanta ba, a gasar cin kofin duniya da ke gudana bana a Rasha.
Da dama daga cikin magoya bayan dai sun bukaci Super Eagles na Najeriya da su yi koyi da takwarorinsu na Senegal wajen fidda magoya bayansu kunya.
A ranar Lahadi mai zuwa Senegal za ta fafata da kasar Japan, wadda ke jagorantar rukuninsu na 8 bayan lallasa Colombia da 2-1, yayinda ita kuma Poland za ta fafata da Colombia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu