Isa ga babban shafi
wasanni

Koriya ta yi waje da Jamus a gasar cin kofin duniya

Tawagar kwallon kafar Koriya ta Kudu ta yi waje da Jamus mai rike da kambi a gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha.

A karon farko kenan tun shekarar 1938 da Jamus ke gaza tsallakawa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya
A karon farko kenan tun shekarar 1938 da Jamus ke gaza tsallakawa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya 路透社
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Koriya ta zura kwallaye biyu a ragar Jamus a dai dai lokacin da ake shirin tashi wasan wanda suka fafata a Kazan.

Korea ta Kudu ta jefa kwallaye biyu a mintina na 92 da 96, bayan an kara wa kasashen biyu lokaci bayan kwashe minti 90 ba tare da zura kwallo ko guda ba.

A karon farko kenan tun shekarar 1938 da Jamus ke gaza tsallakawa zuwa matakin zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya, yayin da a bana ta kammala a can kasan teburi a rukunin F.

Ko da dai ita ma Koriya ta Kudu za ta tarkata inata-inata zuwa gida.

Sweden ce ta jagoranci teburin rukunun na F bayan ta casa Mexico da kwallaye 3-0, yayin da kasashen biyu duk suka tsallaka zagaye na biyu na gasar ta cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.