Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo da Messi sun fice daga gasar cin kofin duniya

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun fice daga gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha, bayan da kasashen su suka yi rashin nasara a fafatawar da suka yi a zagaye na biyu na gasar.

Lionel Messi na Argentina da Cristiano Ronaldo na Portugal, bayan wasannin da aka fitar da su daga gasar cin kofin duniya da Rasha ke karbar bakunci..
Lionel Messi na Argentina da Cristiano Ronaldo na Portugal, bayan wasannin da aka fitar da su daga gasar cin kofin duniya da Rasha ke karbar bakunci.. AFP
Talla

A wasan farko da aka fafata a garin Kazan, Faransa ce ta samu nasara akan Argentina da kwallaye 4-3, wanda cikinsa ne tauraruwar dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe ta haska, bayan da dan wasan mai shekaru 19, ya zura biyu daga cikin kwallayen da Faransa ta ci.

Mbappe ya zama dan wasa mafi kankantar shekaru na biyu da ya ci kwallaye 2 a gasar cin kofin duniya, bayan tarihin farko da Pele ya kafa a shekarar 1958 na cin zura kwallayen a gasar cin kofin duniya, lokacin yana da shekaru 17.

A wasa na biyu da aka fafata a birnin Sochi, kasar Uruguay ta samu nasara akan Portugal da kwallaye 2-1, kuma dan wasan kungiiyar PSG Edinson cavani ya zura duka kwallaye 2 a ragar Portugal.

Mai yiwuwa ne dai gasar cin kofin duniyar ta bana ta zama ta karshe da Cristiano Ronaldo zai halarta, la’akari da cewa a 2022 lokacin da Qatar za ta karbi bakunci, Ronaldo zai kai shekaru 37 idan yana raye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.