Isa ga babban shafi
wasanni

Senegal ta fice daga gasar cin kofin duniya

Colombia ta yi nasara kan Senegal da ci 1 mai ban haushi matakin da ya bata damar tsallakawa zuwa zageyen kasashe 16 da za su kara a ci gaba da wasannin cin kofin duniyar da ke gudana a Rasha. Nasarar ta Colombia ya tilastawa Senegal ficewa daga gasar wanda ke nuna cewa dukkanin kasashen Afrika sun kammala ficewa daga gasar tun daga zagayen rukuni-rukuni.

Senegal wadda ke rukunin H ita ce kasa ta biyar da ta wakilci Afrika a gasar cin kofin duniyar da ke ci gaba da gudana a Rasha, inda kuma ta yi rashin nasarar kammala wasannin rukuni-rukunin da maki 4.
Senegal wadda ke rukunin H ita ce kasa ta biyar da ta wakilci Afrika a gasar cin kofin duniyar da ke ci gaba da gudana a Rasha, inda kuma ta yi rashin nasarar kammala wasannin rukuni-rukunin da maki 4. REUTERS/David Gray
Talla

Makin Senegal din dai ya zo dai dai dana Japan wadda Poland ta lallasa da ci daya mai ban haushi, yayinda Colombia ta dare sama da maki 6.

To sai dai alkalan wasa a Rashan sun yi amfani da bambancin adadin katinan gargadin da aka bai wa 'yan wasan da suka fito daga kasashen biyu, inda aka samu cewa an bai wa Senegal katinan har sau 6 yayinda Japan aka ba ta sau 4.

Alkalan wasan sun ce akwai bambancin da'a tsakanin 'yan wasan na Senegal da kuma na Japan, maakin da ke nuna cewa Japan din ce ta cancanci ta ci gaba da zama a gasar ba Senegal ba.

Senegal wadda ke rukunin H ita ce kasa ta biyar da ta wakilci Afrika a gasar cin kofin duniyar da ke ci gaba da gudana a Rasha, inda kuma ta yi rashin nasarar kammala wasannin rukuni-rukunin da maki 4.

Sauran kasashen da suka wakilcin sun hadar da Najeriya da Masar da Morocco da Tunisia, wadanda duk aka fitar da su a wasannin rukuni-rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.