Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar ya sha alwashin horar da Mbappe

Dan wasan Brazil Neymar Junior da ke ci gaba da fuskantar suka bayan mummunar rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya da ta gudana a Rasha, ya ce duk da caccakar da ake masa hakan ba zai hana shi taimakawa Kyllian Mbappe ba wajen horar da shi don ganin ya zama babban dan wasa a idon duniya.

Neymar dai wanda ke matsayin dan wasa mafi tsada a duniya na kallon kanshi a matsaya jagora wajen nasarar da Mbappe.
Neymar dai wanda ke matsayin dan wasa mafi tsada a duniya na kallon kanshi a matsaya jagora wajen nasarar da Mbappe. REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

Neymar dai ya gaza cimma tsammanin da aka yi na dage kofin duniyar a wannan karon matakin da ya haddasa masa ci gaba da shan suka musamman bayan rashin nasara a hannun Belgium da ci 2-1 a zagayen kasashe 8 na gasar cin kofin duniyar.

A cewar Neymar duk da ya yi bakin cikin fitarwar da Belgium ta yi masa daga gasar, amma yaji dadi da yadda abokinsa Kyllian Mbappe ya yi nasarar dage kofin ga kasarsa a karo na biyu.

Neymar dai wanda ke matsayin dan wasa mafi tsada a duniya na kallon kanshi a matsaya jagora wajen nasarar da Mbappe ke samu a yanzu duk cewa tazarar kwallayen da suka zura a raga a kakar da ta gabata bai taka kara ya karya ba.

Neymar din dai ya zura kwallaye 19 ne kadai a wasanni 20 da ya bugawa PSG yayinda takwarin nasa Mbappe ya zura kwallaye 13 a wasa 24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.