Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo zai biya Spain tarar euro miliyan 19

Hukumar lura da tattara harajin kasar Spain ta amince tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya biya euro miliyan 19 a matsayin bashin harajin da ya kaucewa biya, yayin wasanninsa a kasar.

Tsohon dan wasan Real Madrid da ya koma Juventus, Cristiano Ronaldo.
Tsohon dan wasan Real Madrid da ya koma Juventus, Cristiano Ronaldo. REUTERS/Jorge Silva/File Photo
Talla

Masu gabatar da kara a kasar ta Spain, sun ce daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin hukumar harajin kasar da wakilan Ronaldo, har da hukuncin daurin shekaru biyu, da kotu ta yanke kan dan wasan, wanda ba zai tabbata akansa ba.

Hukumomin Spain na yafewa wadanda aka yankewa hukuncin daurin shekaru biyu muddin ya tabbata, karo na farko kenan da aka samesu da laifi, wanda bai shafi haddasa rikici ko tauye hakkin wani ba.

A shekarar 2016, abokin hamayyar Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, ya biya hukumomin kasar Spain tarar euro miliyan 2, sakamakon samunsa da laifin kaucewa biyan wasu kudaden haraji, tare da fuskantar hukuncin daurin watanni 21, sai dai kasancewar karo na farko kenan da aka taba samunsa da laifi a Spain, hukuncin zaman gidan yarin bai tabbata akan dan wasan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.