Isa ga babban shafi
Wasanni

Amfani da kai a kwallo na haifar da matsalar kwakwalwa ga mata

Binciken masana lafiya ya nuna cewa sa wa kwallo kai yayin fafata wasan kwallon kafa, ya na da matukar hadari ga ‘yan kwallo mata, fiye da takwarorinsu maza har ninki fiye da sau biyar.

'Yar wasan kwallon Amurka Morgan Brian (dama) tare da 'yar wasan gaba ta Jamus Alexandra Popp, yayin fafatawa a gasar cin kofin duniya ta 2015 a filin wasa na Olympic a birnin Montreal. 20 ga watan Yuni, 2015.
'Yar wasan kwallon Amurka Morgan Brian (dama) tare da 'yar wasan gaba ta Jamus Alexandra Popp, yayin fafatawa a gasar cin kofin duniya ta 2015 a filin wasa na Olympic a birnin Montreal. 20 ga watan Yuni, 2015. NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images
Talla

Kwararru bisa fannin lafiyar da ke Amurka sun yin amfani da kai wajen tare kwallo ko zurata a raga, ga mata ‘yan kwallo na tatatre da hadarin haddasa musu matsaloli a kwakwalwa.

Micheal Lipton, Farfesa a fannin kula da lafiyar kwakwalwa, na Kwalejin koyon aikin likitanci ta Albert Einstein, ya ce sun samu wannan sakamakon bincike ne, bayan gwajin ‘yan kwallo mata da kuma takwarorinsu maza 49 daga kowanne bangare.

Yayin binciken, masanan sun lura da irin yadda ruwan da ke cikin kwakwalwa kan tabu a duk lokacin da dan wasa ya tare kwallo da kai, ko kuma ya zura ta a raga, inda bincikensu ya tabbatar da cewa, kwakwalwar ‘yan kwallo mata ta fi fuskantar hadarin samun matsala a duk lokacin da suka yi amfani da kai yayin fafata wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.