Isa ga babban shafi
Wasanni

Serena ta sha kaye mafi muni a tarihinta

Seerena Williams ta fuskanci shan kaye mafi muni a tarihin tsawon lokacin da ta shafe tana fafatawa a fagen wasan kwallon tennis.

Tsohuwar lamba 1 a fagen wasan kwallon tennis ajin mata a duniya Serena Williams, 'yar kasar Amurka.
Tsohuwar lamba 1 a fagen wasan kwallon tennis ajin mata a duniya Serena Williams, 'yar kasar Amurka. AFP Photo/Oli SCARFF
Talla

Serena ta sha kayen ne a gasar Tennis ta WTA da ke gudana a San Jose da ke jihar California a Amurka, inda Yohanna Konta ‘yar Birtaniya ta lallasa ta ta kwallaye 6-1 da kuma 6-0, cikin mintuna 51 kacal da soma wasan, abinda ya tilasta ficewar serena daga gasar.

Wannan gasa dai itace ta Farko da Serena ta shiga bayan fafatawa a gasar Wimbledon da aka kammala ta a birnin London, wadda ta kare ta a matakin ta biyu.

Har yanzu dai serena na kan kokarin maido da karsashinta a fagen kwallon tennis bayan da ta gaza haskawa a mafi akasarin lokutan kakar wasan tennis ta 2017, sakamakon haihuwa da ta yi, amma watanni hudu bayan sauka da koma fagen wasa.

A lokacin da ta ke zantawa da manema labarai bayan kammala wasan, Yohanna Konta ta bayyana cewa ba ta zaci zata samu wannan nasara kan Serena, sai dai bayan soma fafatawar, sam Serena ba ta yi kama da shahararriyar ‘yar wasan da ta lashe kofunan wasannin tennis har sau 72 a tarihinta ba.

Kididdiga ta nuna cewa bayan soma wasannin tennis zuwa yanzu Serena ta lashe kyautar kudi zalla sama da Fam miliyan 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.