Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City ta lashe Community Shield

Manchester City ta lashe gasar Community Shield ta Ingila bayan ta casa Chelsea da kwallaye 2-0 kuma Sergio Aguero ne ya jefa dukkanin kwallayen a ragar Chelsea, abin da ya sa aka bayyana shi a matsayin gwarzon wasan na ranar Lahadi.

Sergio Aguero ya taimaka wa Manchester City wajen lashe gasar Community Shield
Sergio Aguero ya taimaka wa Manchester City wajen lashe gasar Community Shield Reuters/John Sibley
Talla

Aguero ya jafa kwallon farko ne a minti na 13 kuma ita ce kwallo ta 200 da ya ci wa Manchester City a tarihi, yayin da ya jefa ta biyu a minti na 58 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Chelsea a karakshin sabon kocinta, Maurizio Sarri, ta rasa samun damar  kaddamar da hare-haren kwallaye a wasan, yayin da sau daya tal ta kaddamar harin cin kwallo mai kyau ta hannun Callum Hudson-Odoi amma Claudio Bravo da ke tsaren ragar Manchester City ya kade kwallon.

An yi fafatawar ce a filin wasa na Wembley kuma a cikin tsananin yanayi na zafi, lamarin da ya sa ‘yan kallo jika kyallaye ko kuma tawul-tawul da ruwa don sanyaya jikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.