Isa ga babban shafi
Wasanni

Ya kamata mogaya bayan United su yi fushi da mu - Pogba

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya ce magoya bayan kungiyar ta su, na da dukkanin dama ko hakkin yin fushi da su, sakamakon yadda kungiyar Brighton ta lallasa su da kwallaye 3-2.

Paul Pogba na kungiyar Manchester United.
Paul Pogba na kungiyar Manchester United. Reuters/Lee Smith
Talla

Wasan na jiya dai ya baiwa manyan abokan hamayyar United a gasar Premier League, damar bata tazarar maki uku kowannensu wato Manchester City, Chelsea da kuma Tottenham.

A baya bayan nan dai Magoya bayan Manchester United tare da wasu tsaffin ‘yan wasan kungiyar, sun bayyana rashin kwarin giwar da suke da shi, dangane da samun nasarar kungiyar a kakar wasa ta bana.

Tsohon dan wasan kungiyar na baya bayan nan da yayi tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki shi ne Paul

Scholes, wanda ya ce ba shakka rashin sayen manyan ‘yan wasa sai sa United fuskantar matukar wahala a kokarin ta na lashe kofuna a bana musamman ma na Premier.

Zalika dan wasan gaba na United Alexis Sanchez, ya ce tilas kungiyar tasa ta sayo ‘yan wasa kwatankwacin Arturo Vidal da Barcelona ta saya a baya bayan nan, idan har tana son lashe kofuna a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.