Isa ga babban shafi
Wasanni

Ko wacce kungiya ce za ta lashe kofin zakarun Turai a bana?

Yau ake komawa fagen gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai bayan shafe tsawon kwanaki 115 da Real Madrid ta lashe kofin a kakar da ta gabata bayan ta doke Liverpool a wasan karshe a birnin Kiev.

Cristiano Ronaldo ya taka rawa wajen nasarorin da Real Madrid ta samu a kakar da ta gabata kafin a bana ya koma Juventus wadda ya yi wa wata kyakkyawar ci a bara
Cristiano Ronaldo ya taka rawa wajen nasarorin da Real Madrid ta samu a kakar da ta gabata kafin a bana ya koma Juventus wadda ya yi wa wata kyakkyawar ci a bara Alberto PIZZOLI / AFP
Talla

Tuni masharhanta suka fara fashin-baki game da makomar Real Madrid a gasar ta kakar bana bayan ta raba gari da Christiano Ronaldo da Zinedine Zidane da suka taimaka wa kungiyar lashe kofin gasar sau uku a jere.

Masharhanta na ganin cewa, kungiyoyi da dama kamar su Liverpool da Barcelona da PSG da Juventus da sauransu duk sun daura damara sosai don ganin sun bai wa mara da kunya.

Ronaldo wanda ya koma Juventus daga Real Madrid, ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallaye a kakanni 6 da suka gabata na gasar ta zakarun Turai, in da a bana ake ganin babu shakka zai yi iya bakin kokarinsa don ganin ya sake kafa wani sabon tarihi a sabuwar kungiyar tasa.

Shi ma Lionel Messi na Baracelona ya daura damarar tunkarar gasar ta bana, musamman idan aka yi la’akari da jawabin da ya yi wa magoya bayansa a Camp Nou da ke nuna cewa, ya ji radadin abin da Roma ta yi musu a bara har ta fitar da su a matakin wasan dab da na kusan karshe a bara.

A bangaren Liverpool kuwa, Mohamed Salah da aka karya masa kafada a wasan karshe a bara, zai yi kokarin ganin a bana ya sake jagorantar kungiyarsa wajen kama hanyar lashe kofin gasar.

PSG ma dai za ta iya tabuka abin kirki a wannan lokaci kamar yadda hasashen masa ya nuna, amma duk da haka ana iya cewa, ba a sanin ma ci tuwo sai miya ta kare.

Fafatawar da za a yi tsakanin Liverpool da PSG a yau Talata za ta yi zafi sosai, lura da zaratan ‘yan wasan da aka tara a kowanne bangare.

Liverpool na tinkaho da Mohamed Salah da Sadio Mane da Roberto Firmino da kowannensu ya jefa kwallaye 10 a raga a kakar gasar ta zakarun Turai da ta gabata.

Ita kuwa PSG na da zaratan ‘yan wasa irinsu Neymar da Kylian Mbappe da kuma Edinson Cavani.

Sauran wasannin da za su dauki hankula a yau sun hada da karawar da za a yi tsakanin Barcelona da PSV Eindhoven da kuma wasan da Tottenham za ta yi da Inter Milan. Sai barje gumin da za a yi tsakanin Monaco da Atletico Madrid.

A bana dai za a gudanar da wasan karshe ne na gasar ta cin kofin zakarun nahiyar Turai a birnin Madrid na Spain, wato birnin da ya fi lashe kofin wannan babbar gasa a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.