Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta tsallaka kwata final a gasar kwallon kwando ta duniya

Najeriya ta zama kasa ta farko daga nahiyar Afrika da ta samu nasarar kaiwa matakin wasan kwata final, a gasar cin kofin duniya na kwallon Kwando, ajin mata da ke gudana a kasar Spain.

'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya D'Tigress.
'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya D'Tigress. The Guardian Nigeria
Talla

‘Yan kwallon kwandon Najeriyar, D’Tigress sun samu matakin na gaba ne, bayan samun nasara kan Girka kwallaye 57-56.

To sai dai masu iya magana sun ce wuyar aiki ba’a fara ba, domin kuwa a ranar Juma’ar nan ‘yan kwallon kwandon na Najeriya D’Tigress, za su fafata da masu rike da kofin duniyar na kwallon kwandon wato Amurka, a wasan zagayen kuda da na karshe.

A halin yanzu dai mafi akasarin masu bibiyar gasar cin kofin duniyar na kwallon kwandon, na kallon wasan na gobe da Najeriya za ta Fuskanci Amurka a matsayin mafi wahala da za ta buga a bana, la’akari da irin tarihin bajintar da Amurka ke nunawa a fagen kwallon Kwando.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.