Isa ga babban shafi
Wasanni

Zai yi wahala a samu wanda zai maye gurbin Ronaldo - Juventus

Darakatan wasanni a Juventus Fabio Paratici, yace zai yi wahala a iya samun wanda zai iya maye gurbin zakakurin dan wasa kamar Cristiano Ronaldo.

Cristiano Ronaldo, yayinda yake murnar zura kwallonsa ta farko cikin gasar Seria A, a ragar kungiyar Sassuolo.
Cristiano Ronaldo, yayinda yake murnar zura kwallonsa ta farko cikin gasar Seria A, a ragar kungiyar Sassuolo. REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Paratici ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar kyautar girmamawa ta mafi kwazon daraktan wasanni a tsakanin takwarorinsa da ke kungiyoyon gasar Seria A, a kasar Italiya.

Yayin da yake zantawa da manema labarai dangane tasirin sauyin shekar Ronaldo zuwa Juventus daga Real Madrid, Paratici, yace kungiyar za ta cigaba da marawa Ronaldo baya domin kare mutuncinsa, dangane da zargin aikata fyade da wata mata ke yi masa.

Darakatan wasannin na Juventus, ya kuma musanta rahotannin dake cewa, kungiyar na shirin maido da tsohon dan wasanta Paul Pogba, wanda a yanzu yake bugawa Manchester United wasa, bayan sauyin sheka zuwa kungiyar daga Juventus a shekarar 2016, kan kudi fam miliyan 89.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.