Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta fafata wasanni 17 ba tare da rashin nasara ba

Pierre-Emerick Aubameyang ya taimakawa Arsenal wajen ci gaba da kare kimarta na rashin shan kaye a wasannin gasar Premier da Europa 17 da ta fafata zuwa yanzu, bayan rashin nasarori sau 2 da ta fuskanta a farkon kakar wasa ta bana.

Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang.
Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang. Reuters/Tony O'Brien
Talla

Aubameyang ya jefa kwallo ta biyu a ragar Bournemouth a wasan da suka tashi 2-1 a ranar Lahadi.

Tun bayan rabuwa da Borussia Dortmund zuwa Arsenal a watan Janairu, Aubameyang dan kasar gabon ya ci wa kungiyar kwallaye 8, ya kuma taimaka mata wajen cin wasu kwallaye 15, daga cikin jimillar wasanni 26 da ya buga mata.

Yayin wasan na Jiya dai kocin Arsenal Unai Emery ya ajiye dan wasansa na tsakiya Mesut Ozil a benci, yayinda kuma ya jagoranci wasan ba tare da dan wasansa nag aba Alexander Lacazette ba saboda fama da rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.