Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool za ta iya lallasa kowace kungiya a duniya - Guardiola

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola, ya ce tilas a amince cewar yanzu haka Liverpool ka iya kasancewa kungiyar da babu kamarta a fagen kwallon kafa na nahiyar turai da ma duniya.

Mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola. REUTERS/Phil Noble
Talla

Guardiola ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai jim kadan bayan samun nasarar da Manchester City ta yi kan Southampton da kwallaye 3-1 a ranar Lahadi, inda ya ce a halin yanzu, Liverpool na tattare da hazakar da za ta iya lallasa duk wata kungiya da za ta ci karo da ita.

Idan Liverpool ta yi nasarar lashe kofin gasar Premier ta bana, zai zama karo na farko da za ta yi hakan tun bayan shekarar 1990.

A karshen makon da ya kare ne dai Liverpool ta lallasa Arsenal da kwallaye 5-1, wadda a yanzu ke jagorantar gasar ta Ingila da maki 54, Manchester City na biye da maki 47, sai kuma Tottenham a matsayi na uku da maki 45, biye da ita kuma Chelsea da maki 43.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.