Isa ga babban shafi
Wasanni

La Liga ta kafa sabon tarihin karuwar adadin masu kallonta

Gasar La Liga ta kafa tarihin jan hankalin karin masu kallon wasanninta da adadi mafi yawa a tarihin kafuwarta.

Shugaban gasar La Liga ta Spain Javier Tebas. 2/10/2018.
Shugaban gasar La Liga ta Spain Javier Tebas. 2/10/2018. REUTERS/Paul Hanna
Talla

Kididdiga ta nuna cewa daga farkon kakar wasa ta bana zuwa tsakiyarta da aka kai, ‘yan kallo miliyan 7 da dubu 520 da 225 ne suka fita zuwa filayen kwallon kafar kungiyoyin da ke buga wasanni, a babbar gasar Spain ta La Liga Santander, da kuma karamar gasar ta La Liga wadda ake kira da Segunda.

Tarihi dai ya nuna cewa, tun bayan kafuwar gasar La Liga a shekarar 1929, adadin masu kallon wasanninta bai taba kaiwa miliyan bakwai ba, amma a kakar wasa ta bana, yawansu ya zarta adadin, bayan samun karin masu kallo dubu 602 da dari 372.

Masu shirya gasar La Ligar ta Spain dai, na kokarin cimma nasarar ganin yawan masu kallonta ya karu zuwa miliyan 15 a karshen kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.