Isa ga babban shafi
wasanni

Manchester United na burin lashe kofuna da dama

Kocin rikon kwarya na Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce, kungiyar ba za ta tsaya a iya matakin ‘yan hudun saman teburin gasar firimiyar Ingila ba, domin kuwa burinta shi ne lashe kofuna da dama.

Ole Gunnar Solskjaer, kocin rikon kwarya a Manchester United ya lashe dukkanin wasannin da ya jagoranci kungiyar
Ole Gunnar Solskjaer, kocin rikon kwarya a Manchester United ya lashe dukkanin wasannin da ya jagoranci kungiyar Svein Ove Ekornesvaag / NTB SCANPIX / AFP
Talla

Kawo yanzu, Manchester United na a matsayi na shida a tebutin gasar, in da Liverpool mai jan ragama ta ba ta tazarar maki 16, amma United din na bukatar maki hudu ne kacal kafin shiga jerin kungiyoyin hudun saman teburi.

Kalaman Solskjaer na zuwa ne bayan kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce, kasantuwar kungiyarsa cikin jerin ‘yan hudun saman teburi, sannan kuma a ci gaba da damawa da ita a gasar zakarun Turai, hakan ya fi muhimmanci a gare shi fiye da lashe kofuna.

Solskjaer ya samu nasara a dukkanin wasannin da ya jagoranci Manchester United tun bayan maye gurbin Jose Mourinho, yayin da kuma ake ci gaba da damawa da kungiyar a gasar FA da kuma gasar zakarun nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.