Isa ga babban shafi
Wasanni

Jami'an ceto sun zakulo gawar Emiliano Sala daga baraguzan jirgi

‘Yan sandan Birtaniya sun ce likitoci sun tantance gawar da jami’an agaji suka zakulo daga cikin baraguzan jirgin saman da ya fada ruwa dauke da sabon dan wasan kungiyar Cardiff City Emiliano Sala.

Hoton sabon dan wasan Cardiff City Emiliano Sala, da jirgin saman dake dauke da shi yayi hadari.
Hoton sabon dan wasan Cardiff City Emiliano Sala, da jirgin saman dake dauke da shi yayi hadari. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Bayan kammala bincike dai a karshe likitoci sun tabbatar da cewa gawar da aka zakulo ta Emiliano Sala ce.

Sama da makwanni biyu da suka gabata karamin jirgin saman da ke dauke da Sala da kuma matukin jirgin David Ibbotson ya fada cikin ruwa a gaf da tsibirin Guernsey da ke Birtaniya, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Cardiff daga Nantes domin fara wasa a kungiyarsa ta Cardiff City bayan sauyin sheka daga Nantes.

A farkon makon nan aka gano baraguzan jirgin saman da yayi hadari da taimakon wani kamfanin jami’an ceto mai zaman kansa. Bayan kammala binciken hukumomin Birtaniya da na Faransa ba tare da gano jirgin da ya bace bane, Iyalan Emiliano sala da wasu ‘yan kwalon kafa na nahiyar Turai, suka tara kudade domin ci gaba da aikin neman inda jirgin ya fada.

Hukumar bincike kan hadurran jiragen sama ta Birtaniya, ta ce jami’anta sun yi kokarin ciro jirgin saman da yayi hadari, daga cikin ruwan da ya fada, amma rashin kyawun yanayi ya sa tilas suka dakatar da yunkurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.