Najeriya ta rasa matsayi na uku a gasar cin kofin Afrika
Najeriya ta rasa damar samun matsayi na uku a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta matasa ‘yan kasa da shekaru 20, wadda kasar Nijar ke karbar bakunci.
Wallafawa ranar:
Najeriya ta fafata wasan neman mataki na uku ne da Afrika ta Kudu, wanda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da suka shafe mintuna 90 da karin lokaci ba tare da kowa ya jefa kwallo a ragar dan uwansa ba.
A zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne Afrika ta Kudu ta samu nasara kan Najeriya da kwallaye 5-3.
Duk da rashin nasarar dai Najeriya ta samu tikitin halartar gasar cin kofin duniya ajin matasa ‘yan kasa da shekaru 20 ta wannan shekara, da kasar Poland za ta karbi bakunci a watan Mayu.
Da yammacin Yau Lahadi za a buga wasan karshe tsakanin Senegal da Mali a filin wasa na Seynu Kounche da ke Yamai babban birinin Jamhuriyar Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu