Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ba ta yin adalci wajen zabar gwarzon dan wasan Afrika

Tsohon dan wasan Super Eagles ta Najeriya, da ke buga bangaren tsakiya, Edema Fuludu, ya ce akwai gyara kan tsarin da hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Afrika CAF ke bi, wajen tantance gwarzon dan wasan nahiyar.

Shugaban Hukumar CAFAhmad Ahmad yayin karrama dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah.
Shugaban Hukumar CAFAhmad Ahmad yayin karrama dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah. AFP
Talla

Fuludu, ya yi tsokaci kan hukumar ta CAF ce, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, kwana guda bayan da Muhammed Salah dan kasar Masar da ke kungiyar Liverpool a Ingila, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afrika, a ranar Talata 8 ga watan Janairu 2019.

A cewar tsohon dan wasan na Najeriya, ya kamata hukumar CAF ta rika zabar gwarzon Afrika daga cikin wasannin da take shiryawa a Nahiyar kadai, ba tare da la’akari da wasannin Turai ba.

Edema Fuludu ya ce, ta hanyar bin shawararsa ce kawai, CAF za ta rika yi wa ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Afrika adalci, amma ba a koda yaushe a rika karrama ‘yan wasan da ke buga gasannin nahiyar Turai ba.

Edema Fuludu na cikin ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya, da suka lashe kofin gasar Afrika a shekarar 1994, da kasar Tunisia ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.