Isa ga babban shafi
wasanni

Barcelona ta casa Real Madrid a Copa del Rey

Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta casa babbar abokiyar hamayyarta wato Real Madrid da kwallaye 3-0 a karawar da suka yi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin Copa del Rey.

Luis Suárez ya zura kwallaye a karawarsu da Real Madrid a ranar Laraba a gasar Copa del Rey
Luis Suárez ya zura kwallaye a karawarsu da Real Madrid a ranar Laraba a gasar Copa del Rey REUTERS/Paul Hanna
Talla

Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar zuwa matakin wasan karshe a gasar kuma a karo na shida kenan a jere da take zuwa wannan mtaki.

Yanzu haka Barcelona za ta hadu da kodai Real Betis ko kuma Valencia a wasan karshe na gasar ta Copa del Rey da za su yi a ranar 25 ga watan Mayu.

Yau ne za a san wacce za ta samu gurbin a wasan na karshe tsakanin Valencia da Real Betis.

A bangare guda, hankula za su karkata kan haduwar da Real Madrid da Barcelona za su sake yi a rabar Asabar mai zuwa amma a gasar La Liga a Bernabeu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.