Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar Premier ta Ingila a karshen mako

Wasan da aka tashi canjaras 0-0 babu ci tsakanin Liverpool da Everton, ya baiwa Manhester City damar darewa sama teburin gasar Premier da maki 71, bayan samun nasara ka Bournemouth da 1-0.

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah lokacin da yayi hasarar damar jefa kwallo a ragar Everton sau biyu a gasar Premier.
Dan wasan Liverpool Mohamed Salah lokacin da yayi hasarar damar jefa kwallo a ragar Everton sau biyu a gasar Premier. AFP/Oli SCARFF
Talla

A halin yanzu Liverpool ce ta biyu a gasar da maki 70.

A sauran wasannin kuma da aka buga na gasar ta Premier a karshen mako, dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku, ya taimakawa kungiyar wajen samun nasara kan Southampton da kwallaye 3-2 a filin asa na Old Trafford ranar Asabar.

Kwallon da Lukaku ya jefa a minti na 89 ya baiwa United damar darewa matakin kungiya ta 4 a gasar Premier da maki 58, yayinda Arsenal ta koma ta 5 da maki 57.

A halin yanzu dai Manchester United ta fafata wasanni 15 a jere, ba tare da rashin nasara ba a gasar ta Premier Ingila, tun bayan da Ole Gunna Solskjaer ya karbi ragamar horar da kungiyar, daga hannun Jose Mourinho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.