FA ta ci tarar mai horar da kungiyar Liverpool
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar kocin kungiyar Liverpool Jurgen Klopp fam dubu 45,000, bayan samunsa da laifin furta kalaman batanci ga alkalin wasa Kevin Friend da ya busa wasansu da West Ham a ranar 4 ga watan Fabarairu.
Wallafawa ranar:
Yayin wasan na gasar Premier da aka tashi 1-1 tsakanin Liverpool da West Ham, Jurgen Klopp ya zargi alkalin wasa Kevin Friend da nuna fifko ga bangaren West Ham.
Ko a watan Disambar, an ci tarar Klopp euro dubu 8000, bayan da ya bazama cikin filin wasa don taya ‘yan wasansa murna, bayan samun nasara kan Everton a mintunan karshe na fafatawar da suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu