Isa ga babban shafi
Wasanni

Kayen da muka sha a hannun United ya hanani barci - Mbappe

Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe, ya ce fitar da su daga gasar Zakarun nahiyar Turai da Manchester United ta yi, ya haddasa mishi matsalar rashin samun isasshen barci saboda damuwar da ya shiga.

Kylian Mbappe, dan wasa gaba na kungiyar PSG.
Kylian Mbappe, dan wasa gaba na kungiyar PSG. REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

A ranar Larabar makon da ya gabata, Manchester United lallasa PSG da kwallaye 3-1 a Paris, a zagaye na biyu a matakin kungiyoyin 16 na gasar ta Zakarun Turai, bayan da a  zagaye na  farko PSG ta yi tattaki zuwa gidan United ta kuma samu nasara kanta da kwallaye 2-0.

Mbappe ya bayyana matakin alkalin wasa na amfani da fasahar maimacin bidiyo wajen baiwa United damar Jefa kwallo ta uku, ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida a mintunan karshe, a matsayin hukuncin da ya girgiza kungiyar ta PSG, la'akari da cewa bai cancanci a baiwa United damar ba.

Sai dai duk da haka, Mbappe, wanda aka sha alakanta da shi da sauyin sheka zuwa manyan kungiyoyi da suka hada da Barcelona da Real Madrid, ya ce zai ci gaba da kasancewa tare da kungiyarsa, duk rashin nasarar kaiwa zagayen kwata final a gasar zakarun turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.