Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta bayyana wadanda take fatan su maye gurbin Suarez

Barcelona ta tsaida shawara kan ‘yan wasan da take ganin sune za su iya maye gurbin dan wasanta na gaba Luis Suarez mai shekaru 32, wanda a yanzu haka ke kusantar lokacin rabuwa da kungiyar.

Gasar La Liga: Luis Suarez yayin murnar jefa kwallaye 3 a ragar Girona.
Gasar La Liga: Luis Suarez yayin murnar jefa kwallaye 3 a ragar Girona. Reuters
Talla

A shekarar 2014 Surez ya koma Barcelona daga Liverpool, wanda kuma ya bada muhimmiyar gudunmawa ga kungiyar ta Barcelona wajen lashe kofuna da dama.

A kakar wasa bana Luis Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye 18 a wasannin La Liga 27.

‘Yan wasan da Barcelona za ta saya don maye gurbin Suarez a cewar hukumar gudanarwar kungiyar, sun hada da Marcos Rashford dake Manchester United mai shekaru 21, dan wasan gaba na Atletico Madris Antoine Griezmann sai kuma dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar kasar Serbia, Luka Jovic

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.