Najeriya ta samu nasarar doke Masar karon farko cikin shekaru 29
Najeriya ta doke Masar da 1-0, a wasan sada zumuncn da suka buga ranar Talata, 26 ga watan Maris, a filin wasa na Stephen Keshi dake Asaba, a jihar Delta.
Wallafawa ranar:
Sabon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Paul Onuachu ne ya jefa kwallon daya tilo a mintin farko da soma wasan.
Rabon da Najeriya ta samu nasarar doke Masar a wasan kwalon kafa tun a shekarar 1990, yayin gasar cin kofin nahiyar Afrika, hakan tasa nasarar ta jiya ke da muhimmanci ga Najeriya, duk da cewa a wasan sada zumunci ta samu.
Manyan ‘Yan wasan Masar da suka hada da Muhd Salah, Ahmed Hegazi da Elmohamady basu samu halartar wasan na jiya Talata ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu