Isa ga babban shafi
Wasanni

Twitter za ta gana da Pogba kan cin zarafin da aka yi masa

Kafar sadarwar Twitter za ta gana da dan wasan Manchester United, Paul Pogba biyo bayan zagin cin mutunci da kuma nuna wariyar launin fata da aka yi masa.

Paul Pogba.
Paul Pogba. Reuters
Talla

Pogba ya zamo dan wasa na uku da aka ci zarafinsu a cikin mako guda a shafukan sada zumunta, bayan ya barar da bugun fanariti a wasansu da Wolves.

Da dama daga cikin abokan taka ledar Pogba sun yi tur da wannan caccakar, yayinda mai horar ta tawagar matan Ingila, Phil Neville ya bukaci ‘yan wasan kwallon kafa da su kaurace wa shafukan sada zumunta baki daya.

A yanzu dai, Dandalin Twitter ya ce, zai gana da masu ruwa da tsaki domin nuna musu irin matakan da suke dauka don magance wannan matsalar ta cin zarafi.

Rashin zura kwallon Pogba ne ya sa Manchester United ta tashi kunnen doki 1-1 da Wolves a gasar firmiyar Ingila, abinda ya bakanta wa magoya bayanta rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.