Isa ga babban shafi

Neymar na gab da daina fuskantar suka daga magoya bayan PSG

Neymar Junior na iya daina fuskantar suka da kyamar da magoya bayan PSG ke nuna masa bayan nasararsa ta zura kwallo guda da ya bai wa Club din damar lallasa Lyon har gida da kwallo daya mai ban haushi.

Dan wasan PSG Neymar Jr.
Dan wasan PSG Neymar Jr. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Ana saura minti 3 a tashi daga wasa ne Neymar dan Brazil mai shekaru 27 ya yi nasarar zura kwallon, kwatankwacin yadda ya yi a makon jiya yayin wasansu da Strassbourg kwallon da ta toshe bakin ‘yan kallon da ke nuna kyama ga Neymar tun bayan shirinsa na sauya sheka zuwa tsohon Club dinsa Barcelona.

Neymar wanda bai samu damar taka leda a wasan da PSGn ta lallasa Real Madris da kwallaye 3 da banza baa gasar cin kofin zakarun turai, sanadiyyar haramcin wasannin gasar da yake fuskanta, manajan Club din Thomas Tuchel ya ce dan wasan yanzu ya hakura kuma yana bayar da gudunmawa dari bisa dari don nasarar Club din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.