Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta gabatarwa da PSG sabon tayi kan Neymar

Tauraron kungiyar PSG Neymar na ci gaba da jiran tsammani kan tabbatar burinsa na yiwa tsohuwar kungiyarsa Barcelona kome, kafin rufewar hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa a farkon watan Satumba.

Dan wasan PSG Neymar Jr.
Dan wasan PSG Neymar Jr. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Jaridar wasanni ta L’Equipe dake Faransa ta rawaito cewar, yanzu haka Barcelona ta gabatarwa da PSG sabon tayin sake kulla yarjejeniya da Neymar kan euro miliyan 160, a biya biyu, tare da kuma mika karin dan wasa guda ko kuma guda biyu.

‘Yan wasan da Barcelona ke son mikawa PSG kuwa sun hada da Ivan Rakitic, sai kuma Ousamne Dambele, wanda Barcelonan tayi tayin mika shi a matsayin aro ga kungiyar ta PSG.

Sai dai rahotanni sun ce tuni Dembele mai shekaru 22 ya noke kan amsa bukatar zuwa PSG a matsayin aro, abinda yasa wasu ke ganin abin da kamar wuya tabbatuwar yarjejeniyar ta sake komawar Neymar Barcelona, har ma da abokiyar hamayyarta Real Madrid da a baya ta yi tayin biyan euro miliyan 100 da ‘yan wasa uku kan tauraron na PSG.

A tsawon shekaru 2 da yayi a gasar Ligue 1, Neymar ya ci wa PSG kwallaye 51, daga cikin wasanni 58 da ya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.