Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya amayar da abin da ke cikinsa kan kyautar FIFA

Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo wanda bai halarci bikin karrama Lionel Messi a matsayin gawrzon dan wasan shekara a bana ba, ya amayar da abin da ke kunshe a cikinsa bayan ya rasa kyautar a wannan karo.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo REUTERS/Massimo Pinca
Talla

A wani sako da ya wallafa tare da hotansa a shafin Instagram, Ronaldo ya bayyana hakuri da juriya a matsayin abubuwan da ke banbance kwararre da dan koyo.

A cewar Ronaldo " duk abin da ya bunkasa a yau, babu shakka ya fara ne daga karami. Ba za ka iya yin komai ba, amma kuma ka aikata komai domin ganin burinka ya cika."

"Sannan kuma ka kwan da sanin cewa, komin dare, gari zai waye". A cewar Ronaldo wanda aka bayyana kalamansa tamkar na masana falsafa.

A karo na shida kenan da babban abokin hamayyarsa a fanin tamaula, wato Messi na Barcelona ke lashe wannan kyauta ta Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, yayin da Ronaldo ya lashe sau biyar.

Kodayake da dama daga cikin masoya kwallon kafa sun yi korafi kan nasarar Messi ta lashe wannan kyauta, inda suke ganin ko ba komai, Virgil van Dijk na Liverpool ya fi cancantar lashe kyautar a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.