Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Rauni zai hana De Gea taka leda a wasan Man United da Liverpool

Da alamu mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United David de Gea ba zai samu damar taka leda a wasan da Club din zai karbi bakoncin Liverpool jagorar Pirimiya a ranar lahadi mai zuwa ba, bayan raunin da ya samu yayin da ya ke dokawa kasarsa kwallo.

David De Gea mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
David De Gea mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Reuters / Andrew Yates Livepic
Talla

De Gea mai shekaru 28 ya samu rauni a kafada ne yayin wasan da suka kara da Sweden karkashin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai ta Euro 2020.

Ana tsaka da wasan ne dai de Gea ya samu raunin a kokarinsa na chafe kwallo matakin da ya sanya maye gurbinsa da Kepa Arrizabalaga da ke taka leda a Chelsea lokacin Spain na da kwallo guda Sweden kuma na nema amma kuma bayan fitarsa Sweden ta samu nasarar zura kwallo yayinda aka tashi wasa canjaras kwallo 1 da 1.

Raunin na de Gea ya zo a dai dai lokacin da Manchester United ke ci gaba da fuskantar koma baya a wannan kaka, kuma rashinsa a wasan daza su karbi bakonci Liverpool zai zamewa Club din babban kalubale musamman ganin yadda kawo yanzu Liverpool ba ta yi rashin nasara a wasa ko guda ba, inda ta ke matsayin jagora a teburin firimiya da maki 24 tazarar maki 8 tsakaninta Manchester City da ke matsayin ta 2.

Matukar De Gea bai samu damar takaleda a wasan na ranar lahadi ba, akwai yiwuwar Manchester United ta yi amfani da mai tsaron ragarta zabi na biyu Sergio Romero dan Argentina don kaucewa shan kaye a wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.