Messi ya sake kafa tarihi a gasar zakarun Turai
Lionel Messi na Barcelona ya zamo dan wasa na farko da ya kafa tarihin zura kwallaye a kakannin wasanni 15 da ya buga a jere a gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da kungiyarsa ta doke Slavia Prague da ci 2-1 a karwarsu a ranar Laraba.
Wallafawa ranar:
Messi ne ya fara jefa kwallon farko cikin minti uku da fara kece rainin bayan ya tattaba kwallo tare da Arthur.
Yanzu haka, Barcelona ce ke jagorantar rukuninsu na F a gasar ta zakarun Turai da maki 7 da ta samu daga wasanni uku da ta buga , in da ta bai wa Inter Milan da Borussia Dortmund tazarar maki 3.
Su ma kungiyoyuin biyu sun fafata da juna a San Siro, inda Inter Milan ta samu nasara da kwallaye 2-0 akan Borussia Dortmund.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu