Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Salon wasan Alcantara bai dace da Liverpool ba - Hamann

Tsohon dan wasan Liverpool Dietmar Hamann, ya ce Thiago Alcantara ba,ya wasa irin na kungiyar, yana mai shawartar koci Jurgen Klopp ya yi kaffa - kaffa da antaya dan wasan da aka saya kan kudi fam miliyan 20 a filin.

tsohon dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara.
tsohon dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara. REUTERS/Eloy Alonso
Talla

Thiago Alcantara ya sanya hannun a kwantiragin shekaru 4 ne da Liverpool daga Bayern Munich ta Jamus a watan Satumban shekarar 2020.

Dan wasan wanda sau 2 yana lashe kofin zakarun nahiyar Turai ya taka rawar gani a Bayern Munich a kakanni 2 na karshe a zamansa a kungiyar, amma kuma ya zabi ya koma Liverpool don fuskantar sabon kalubale.

Sai dai ‘yan watannin da ya shafe a kuniyar ba su kasance yadda yake so ba, sakamakon tsaiko da aka samu saboda annobar Korona da kuma mummunar rauni da ya samu a gwiwa.

Duk da cewa ya murmure ya dawo filin wasa, Hamann yana ganin salon wasansa bai dace da na Liverpool ba, saboda haka yake shawartar Koch Jurgen Klopp da ya rika taka tsantsan wajen sanya shi a wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.