Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan Madrid sun mamaye tawagar da babu kamar ta cikin shekaru 10

Hukumar tattara tarihi da kididdigar lamuran da suka shafi kwallon kafa ta duniya, ta sanya ‘yan wasan Real Madrid da Barcelona guda bakwai na da da na yanzu, cikin tawagar ‘yan kwallon da ta ce babu kamarsu a tsawon shekaru 10 na baya bayan nan.

'Yan wasan Real Madrid Sergio Ramos, Marcelo, Modric da Toni Kroos
'Yan wasan Real Madrid Sergio Ramos, Marcelo, Modric da Toni Kroos Real Madrid CF
Talla

Fitacciyar tawagar dai ta kunshi Sergio Ramos, Marcelo, Luka Modric da Toni Kroos tare da Cristiano Ronaldo, sai kuma Lionel Messi da Andres Iniesta.

Sauran fitattun ‘yan wasan sun hada da mai tsaron raga Manuel Neuer, Philip Lahm, Virgil van Dijik da kuma Robert Lewondokwski da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya na FIFA a shekarar bara.

Hukumar kasa da kasa dake tattara kididdiga da tarihin sha'anin kwallon ta IFFHS, tace ‘yan wasan Real Madrid na da dana yanzu sun fi yawa a fitacciyar tawagar da ta zaba ne, saboda irin nasarorin da kungiyar ta samu na lashe kofin gasar Zakarun Turai su hudu cikin shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.